Spread the love

Gwamnatin jihar Sakkwato ta bayar da sanarwa shirin da take da shi na gina  madatsun ruwa(Dam)har guda uku a wuaren da ruwa suka fi yin barna.

Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da hakan a lokacin da yakai ziyarar jaje ga wadanda suka samu ambaliyar ruwa a karamar hukumar Kebbe da Silame.

Ya ce gina madatsun ruwa a wuraren zai takaita samun ambaliya kamar yadda ta faru  a yanzu.

A cewarsa gwmnati ta kammala shirin samar da madatsar ruwa  a karamar hukumar Rabah.

A lokacin ziyarar ya zagaya a dukkan gadoji da ruwa suka barnata  abin da ya kai su ga faduwa, akwai gada a Silame da Kawa da Romon sarki da Romon Liman da Kebbe da Tambuwal duk a cikin kananan hukumomi 10 da ruwa suka yi ambaliya.

Gwamnan ya jajanta masu ya kuma gargade su da su rika samar da hanyoyin ruwa da sauraren shawarar masana don ita kadai za ta tseratar da su da dukiyoyinsu ga samun ambaliyar ruwa.

Gwamna ya sanar cewa gwamnati za ta bayar da tallafi na musamman da don bunkasa noman rani wanda hakan zai rage radadin hasarar da ka samu a jiha.

Haka ya ba da sanarwa gwamnati  za ta taimaka ga abubuwan jinkai ga wadan da suka samu hasara kuma za ta turo masana su kididdige hasarar da aka yi kuma su samar da hanyar kare faruwar lamarin a gaba.

Dubban mutane ne ruwa suka kora daga gidajensu da gonakinsu da filayensu a jihar Sakkwato, karamar hukuma 10  daga cikin 23 ne ruwa suka yanke daga shigowa babban birnin jihar Sakkwato kai tsaye, sai sun zagaya a wasu garuruwa na daban. 

Kananan hukumomin da ambaliya ta mamaye na bukatar gwamnati ta gyara masu gadoji da hanyoyinsu da suka lalace cikin gaggawa domin su rage radadin hasarar da suka samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *