Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Shugaban Jam’iyyar APC reshen jihar zamfara, Alhaji Lawal Muhammad Liman ya yi kira ga Sufeto Janar na ’Yan sanda, Mohammed Adamu da cewa ya gaggauta kafa kwamitin bincike na musamman kan abin da ya bayyana matsayin cin mutunci da ba ta suna da cin zarafi tare da tsoratar da mambobin jam’iyyar APC da ‘yan sandan ke yi babu gaira babu dalili a karkashin jagorancin Kwamishinansu jihar Usman Nagoggo.

Shugaban jam’iyyar ya yi wannan kiran ne a wani taron da ya kira na manema labarai a ofishinsa dake Gusau babban birnin jiha, lokacin da yake mayar da martani dangane da irin cin zarafin da ake yi masu, na hana su hakkinsu na na walwala da ‘yan sandan jihar ke yi.

Ya kara da cewa, kiran ya zama dole sakamakon ganin yadda, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Usman Nagogo ya hada baki da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya kame mambobin APC 17 kuma aka tsare su ba bisa ka’ida ba fiye da awanni 10 tare kuma da sakinsu babu wani sharadi.

Liman ya ci gaba da cewa, jam’iyyar ta sanar da dukkanin masu ruwa da tsaki kan lamarin a matakan kasa kan matakan gaggawa da za a dauka don tabbatar da lafiyar dukkan mambobin jam’iyyar a jihar.

A cewarsa, mambobin jam’iyyar za su ci gaba da kasancewa ‘yan kasa masu bin doka tare da gargadin mambobinsu da su guji duk wani nau’i na karya doka da oda da ka iya haifar da rikici a jihar , ya ce shugabancin jam’iyyar zai ci gaba da jajircewa don yaki da ‘yan cinsu na halal.

Da yake kare gwamnati darakta janar na fannin harkar yada labarai, a fadar gwamnatin jihar Zamfara, Alhaji Yusuf Idris Gusau, ya nisanta gwamnatinsu da wannan zargin da ake yi masu, yace wannan matsala ce tsakanin su da jami’an tsaro.

Hakama yace suna kokarin shafawa gwamnati kashin kaji ne kawai, domin wannan zargin ba yada tushe balle makama, domin ba tsakanin APC da PDP ake wannan kai ruwa rana ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *