Gamayyar kungiyoyi fararen hula 180 a Kano sun yi Allah wadai da karin farashin man fetur da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi daga 148 zuwa naira 151 akan kowace lita.

Shugaban hadaddiyar kungiyar kwamared Ibrahim A. Wayya ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano,

Kwamred wayya ya ce abin takaici ne kwarai idan akai la’akari da yadda talaka ke cikin kunci amma gwamnati ta kara kudin Man fetur da karin wutar lantarki 100 bisa 100.

Haka kuma Kwamared wayya ya nuna takaicinsa akan yadda babban bankin kasa CBN ya kara yawan cajin da ya ke wa masu ajiyar kudi a Bankuna wanda haka zai shafi Talaka da masu karamun karfi,

Ya yi kira da babbar murya akan gwamnati ta dawo da asalin farashin mai da na lantarki, matukar ba’a dawo da farashin ba za su dauki matakin da ya dace a nan gaba.

Kungiyoyi ire-irensu sun fara Kira ga gwamnati Wanda matukar ba ta ji Kiran ba zai iya haifar da zanga-zangar limana wadda tsarin dokar kasa ya aminta da ita, duk wanda yake son ya nuna rashin gamsuwarsa ga wani abu da gwamnati ta yi zai iya gudanar da zanga-zangar limana ba cin zarafi ko kalaman batanci ga kowa, manufa kawai a an karar da gwamnati rashin son abin da ta yi domin ta duba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *