Jam’iyar APC na yunkurin daga babban zabenta har sai zuwa farkon sabuwar shekara ta 2021 sabanin watan Disamba da aka shata gudanar da zaben a farko abin da ya hasala ‘yan jam’iyar.

An zargi za a sabawa yanda aka tsara ne tun a farko na zabar sabbin shugabanni abin da wasu jagororin jam’iyar suka ce ba za su aminta ba har in hakan ta taso.

Mai magana da yawun Mai Mala Buni ya ce wannan maganar ba ta da Makama balle tushe, yanzu ba zaben jam’iya ne gabansu ba zaben Gwamnan jihar Edo da Ondo ne, sai an kammala tukun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *