Spread the love

Daga Aishatu Bashir Tambuwal
aishabasheer2017@gmail.com

Assalamu alaikum, uwargida,Amarya har ma da ‘yan mata, muna muku barka da wannan lokaci, a yau na zo muku da yanda ake had a MIYAR RIDI, ka da ku manta tallenki sirrinki.


MIYAR RIDI


Abubuwan Hadawa

Ridi

Kifi/nama

Tattasai

Albasa

Attarugu

Tumatur


Yadda ake hadawa

Da farko ki wanke ridinki wadatacce kishanya ya bushe.

Sai ki raba biyu, ki nika rabi, ki soya rabi. Ki soya shi har sai ya fara kamshi, sai ki sauke “kar Ki bari yayi baki.”

Sai ki kawo kayan miyarki markadaddu wadatattu ki sa naman ragonki da gyararren kifinki busasshe ki soyasu tare da kayan miyarki, ka da su soyu sosai.

Sai ki tsaida ruwa ki rufe. Idan ya tafasa ya yi kauri sosai sai ki kawo nikakken ridinki ki zuba kisa maggi da curry da gishiri da sauran spices sai ki rufe ki basu kamar minti goma.

Sannan sai ki kawo yankakken ugu leaf, kananan yanka, da yankakkiyar albasa sai ki zuba, ki kawo ridinki soyayye wanda baki nika ba ki zuba ki jujjuya sai ki rufe, bayan minti biyar sai ki sauke.

Za a iya cinta da abinci kamar haka:

 Tuwon shinkafa

Sakwara

Sinasir

Funkasau, da sauransu.

Managarciya na kawo maku kalolin abinci ne domin amfanin al’umma gaba daya, da zimmar ba da gudunmuwa ga kara Zama silar daurewar aure a tsakanin ma’urata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *