Spread the love


Tsohon gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa bai halarci taron zaben  shugabannin PDP da aka gudanar a filin Wasa na Giginya a birnin Sakkwato a jiya Assabar.


Tun kafin soma fara taron an yi ta rade-radin Bafarawa ba zai halarta ba domin an zargi a rabon sabbin shugabbannin bai gamsu da yanda aka raba mukaman ba.

Wannan shi ne karon farko tun bayan da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya shiga jam’iyar PDP ba a ga Bafarawa a babban taron jam’iyar dake da muhimmanci sosai.

Jam’iyar ta zabi sabbin shugabanninta in da ta zabi shugaba na jiha Bello Aliyu Goronyo ya maye gurbin babban na hannun daman Bafarawa Alhaji Ibrahim Milgoma.

An zabi Alhaji Aliyu FC mataimakin shugaba, sai Kuma Sakataren jam’iya Alhaji Zaki Bashire, an zabi Alhaji Murtala Abdulkadir Dan’iya matsayin ma’aji shi ne ya maye gurbin kanen Bafarawa Alhaji Nasiru Bafarawa.

Shugabar mata Hajiya Kulu ‘Yar Sardauna ce jam’iyar ta zaba, sai Mustafa Binji shugaban matasa.

Duk kokarin da Managarciya ta yi na sanin dalilin da ya hana wa Bafarawa halartar taron hakarta ba ta cimma ruwa ba don wayarsa ba ta zuwa a lokacin hada rahoton.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *