Kasar Nijeriya ta bi sahun takwarorinta wajen tunawa da ranar kunar bakin wake ta diniya, in da a Nijeriya akalla akawi mutum 264 da ake da labarin kashe kansu suka yi a cikin shekara hudu a binciken da jaridar daily trust ta yi.

Manufar fitowa da ranar domin a hadu a hana mutane kashe kansu a duniya.

Mutane mata da maza suka kashe kansu daga Junairun 2017 zuwa Agustan nan kamar yadda rahoton ya nuna a tsakanin nan.

Kididdigar ba ta sanya duk wani kisan da ba a bayyana shi a kafofin yada labarai ba.

Kisan kai babban laifi ne a Nijeriya a cikin sashe na 327 na daftarin manyan laifuka, dokar ta bayyana duk wanda ya Yi yunkurin kashe kansa za a yanke masa shekara daya a gidan yari, haka dokar ta tanadar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *