Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Kwamitin da jam’iyyar APC ta kasa ta kafa a jihar zamfara karkashin jagorancin Abdullahi Ja’o Zurmi, domin ladabtar da ‘ya’yan jam’iyyar APC, wayanda suka nuna rashin da’a da biyayya ga jam’iyya, ya fara zaman sa a yau Talata a sakatariyar jam’iyyar APC dake Gusau babban birnin jiha.

Da yake amsa tambaya ga yan jarida, Jim kadan bayan kammala taron na yau, shugaban jam’iyyar APC na mazabar ‘Yar galadima dake garin Anka, Malan Shafi’i Musa, yace sun zo ne domin karba goron gayyatar da uwar jam’iyyar APC tayi masu.

Malan Shafi’i, wanda ya bayyana cewa, su basu da masaniyar cewa, sunayen su na cikin wayanda Sanata Kabiru Marafa ya saka wajen sa kara, adon haka yace su ba ruwan su da wannan zance.

Shugaban wanda keda matsayin shugaban ciyamomin APC na mazabu a kananan hukumomi goma sha hudu, yace idan uwar jam’iyyar APC zata basu dama da zasu kai Sanata Kabiru Marafa tare da Surajo Garba Mai katatako a gaban kuliya domin sunyi amfani da sunayen su ba tare da gaya masu ba.

Ya bayyana cewa, cikin kananan hukumomi goma sha hudu dake ga jihar zamfara, ciyamomin APC na kananan hukumomi tara, da shuwaga bannin mazabu suka amsa goron gayyatar, sauran sun bada dalilan da ya hanasu zuwa.

Haka zalika, ya bayyana cewa su a shirye suke, domin yiwa uwar jam’iyyar su biyayya, adon haka yaja kunnen mutanen sa dasu sani fa, cewa Sanata Marafa yana son watse APC jihar zamfara ne kawai, domin biyan bukatar wasu na da ban.

Ya bayyana dalilan da yasa, yace hakan, domin a ta bakinsa akwai yan Kabiru Marafa da yawa cikin wannan gwamnatin kamar shi Mai katako, da Bala Bello Maru, sakataren gwamnatin jihar zamfara, da sauran matai maka na musamman da dai sauran su.

Anashi jawabi, Malan Adamu Rabi’u Tseku, shugaban jam’iyyar APC na mazabar Bagega, ya bayyana cewa hakika su na biyayya ga uwar jam’iyyar APC, adon haka basusan lokacin da aka saka sunayen suba, saboda haka basu ba tafiyar Kabiru Marafa da Mai katako.

Hakama wani shugaban jam’iyyar APC na mazabar Wuya, Alhaji Aminu Abubakar Wuya, ya bayyana bijirewar su ga tafiyar Kabiru Marafa, yace basu ba wannan tafiyar, domin sun gano cewa yana son watsewar jam’iyyar ne a jihar zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *