Spread the love

Akalla Hausawa mutum biyu ne dake zaune a garin Oyigbo a karamar hukumar Oyigbo ta jihar Rivers suka rasa ransu a wani farmaki da ake zargin ‘yan kungiyar Igbo ta Biyafara(IPOB) suka kai masu a Oyigbo.

Shedun gani da ido ya ce ‘yan kungiyar sun kaddamar da harin a ranar Assabar da lahadi ga Hausawan.

Majiyar ta ce mutum biyu ne suka rasa ransu wasu da dama sun samu mummunan raunuka.

“Lamarin farmakin ya faru ne kamar wanda aka shirya a ranar Assabar ya fadada zuwa lahadi wasu matasan Biyafara ne suka zagaye Hausawa da makamai aka kashe mutum biyu wasu biyu suka samu rauni.” a cewar majiyar.

Mai magana da yawun al’ummar Arewa a jihar Rivers Alhaji Musa Sa’idu ya tabbatar da lamarin ya kuma yi tir da faruwarsa.

Alhaji Musa Sa’idu gawar wadanda aka kashen tana a garin Oyigbo da ake zargin matasan kungiyar sun kashe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *