Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Shugaban hukumar Zakka da wakafi ta jihar Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki a wata tattaunawar da ya yi da Mujallar Managarciya kan yadda gidauniyar Katar Charity  ta raba Akuyoyi 180 a karo na uku ga mabukata da suka samu jarabawar talauci ko rasa mazaje a jihar Sakkwato ya ce kowace mace ta samu akuya biyar da Bunsuru daya domin ta je ta yi kiyo ta ja jari wanda hakan zai rage radadin talauci a yankunan karkara.

  Ya ce sun yi wannan ne bisa ga nazarin da suka yi na akwai bukatar taimakon al’umma don wanda aka yi a farko an samu cigaba kamar yadda bincike ya nuna ‘kan haka ya sa muka sake zabo wadan da suka yi abin kwarai a rabon farko, sai muka bayar da hakuri ga wadan da bas u rike ba, nasarar da kowace gunduma ta samu ne zai sa mu mayar da su abokan tafiyarmu ga wani abu in ya taso.

‘A wannan karon duk wadda aka baiwa akuya hukumar zakka ta ba ta tallafin 5000 don ta soma kula da ita, in suka rika zuwa wata shekara ana son a sayi wasu gare su’ a cewar Maidoki.

Mine ne sirrin da ya sanya gidauniyar Katar ta gamsu da cigaba da aiki da ku? Ya ce “Gaskiya su yafi dacewa a yi wa wannan tambayar, amma nasan shimfidar fuska tafi ta tabarma, sannan nasan tun zuwansu ba mu taba nuna kwadayi ga abinsu ba, mukan sanya namu a duk sanda za su ba da nasu, ba mu yarda mu nuna mu talakawa ne ba,muna kokarin  kare martabar Sakkwato da mutuncinta, kila hakan ya sanya suka gamsu su cigaba da aiki da mu bayan jajircewar mai girma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da Mai martaba sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ga aikin addini.” A cewar Sadaukin Sakkwato Muhammad Lawal Maidoki.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *