Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar zamfara ta sanar da ranar Asabar 5/12/2020, a matsayin ranar da zata gudanar da zaben majalisun kananan hukumomi.

Wannan ya biyo bayan da umurnin da gwamnan jihar zamfara Bello Muhammed Matawalle ya bayar, cewa hukumar zaben ta tabbatar da ta shirya zaben kananan hukumomi, ba tare da bata lokaci ba.

Wannan yana kunshe a cikin wata takardar bayani mai dauke dasa hannun sakataren hukumar Muhammad Sani Halilu Kura, aka rabawa manema labarai a garin Gusau babban birnin jihar.

Bayanin ya kara da cewa, Shugaban hukumar zaben jihar Zamfara Alhaji Garba Muhammad Danburan Gusau, yana farin cikin shedawa jama’a da dukan jam’iyyun dakeda rajista masu neman shiga zaben kananan hukumomi, da jami’an tsaro, da kafafen yada labarai, da kuma dukan masu ruwa da tsaki cewa an tsaida biyar ga watan Disamba na wannan shekara (5/12/2020). Ta zama ranar zabe.

Haka zalika, Danburan Gusau ya nemi goyon bayan jama’a da masu fada aji da dai sauran masu ruwa da tsaki, domin su gadanar da zaben cikin kwanciyar hankali da walwala.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *