Spread the love

Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Nijar a gobe Litinin domin halartan taron shugabannin kasan yankin Afrika ta yamma karkashin gammayar ECOWAS.


Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ranar Lahadi, a shafinsa na kafar sada zumu talk.


Ya ce Buhari zai samu rakiyar manyan ministocinsa kuma zai dawo bayan zaman.
Garba Shehu yace: “Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Niamey, jamhurriyar Nijar domin halartan taron gangamin shugabannin kasar yankin Afrika ta yamma ECOWAS karo na 57.


A taron da za’ayi cikin kwana daya, za’a tattauna kan rahoto na musamman kan cutar Korona da Buhari zai gabatar bayan nada shi gwarzon yaki da COVID-19 a taron yanar gizon da aka yi ranar 23 ga afrilu, 2020.


Hakazalika za’a tattauna kan lamarin ta’addanci  da kuma juyin mulkin da Sojoji sukayi a kasar Mali.


Bayan kammala taron ana sa ran shugaba Buhari ya dawo Nijeriya kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *