Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir. 

Zaben shugabannin PDP na kanan hukumomi da aka gudanar a jihr Sakkwato ya bar baya da kura domin wasu ‘yan takara sun koka da yanda aka yi zaben suna ganin ba a yi adalci ba ko kadan.

Alhaji Kasimu  Ummarun Kwabo dan galadiman Jarman Sakkwato yana cikin ‘yan takarar neman kujerar shugaban karamar hukuma da aka yi wa rashin adalci ya kira manema labarai don nuna rashin gamsuwarsa da zaben da aka yi, ya ce a hakikanin gaskiya gwamna da dattijan jam’iya sun ce a je kowace karamar hukuma  a zauna da kowane bangare a shirya yadda  za a kassafa shugabannin, a Sakkwato ta Arewa amma ba a kira ba, sai da lokaci ya kure kuma ba adalci azaman.

“A mazabata ta magajin gari B ne aka ce za a zabi shugaba, an sanya babban sakatare da babban darakta da sakataren karamar hukuma da daya dan takara suka yi magana dani don janyewa ban aminta ba, ni zan shiga zabe, don sun sabawa maganar gwamna.

“A ranar zabe sun shirya hana mu shiga wurin zabe, haka aka yi mun zo aka ce sai wanda yake da abin ratayawa a wuya don sun san ba su bamu ba, don kada mu kawo wata rigima a wurin muka je muka yi namu zaben shugabanni a bangaremu kuma mun ba da sunayen a hannun jam’iya.” a cewar dangaladiman jarma.

Ya ce ba wanda ya yi silhu a zaben, su ba su aminta ba, hasalima zaben an yi shi ne ba tare da an sayar da fom na takara ga ‘yan takara ba sai an yi matsaya gare ka sannan a baka fom ka cika.

“Fom baya wurin uwar jam’iya ko yana can ba’a bayar da dama a sayarwa kowa ba, a shirye muke in an bayar da dama mu saye a duk Sakkwato ba wanda ya saye ko aka baiwa fom na takara, nasan da haka don ni jigo ne a jam’iyar PDP.” in ji Kasimu Ummarun Kwabo.

Ya yi fatan Gwamna Tambuwal ya shiga lamarin don a yi gyara mutane su zabi wanda suke so shi ne daidai a harka ta siyasa in za a yi abu a yi bisa cancanta.

Sanata Ibrahim Danbaba Dambuwa wanda shi ne ya jagoranci zaben a karamar hukumar Sakkwato ta Arewa ya ce an gudanar da zabe lafiya ba korafi ga kowa mutane sun amince da abin da ya faru.

Ya ce abin da ya faru anan ‘yar manuniya ce ga sauran kananan hukumomi don tabbatarwa ne a sauran suma, bai samu wani korafi ga kowa ba sun gama zabe lafiya. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *