Spread the love

Tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce abin da gwamnatin tarayya ta yi wajen farfado da tattalin arzikin kasa ya yi daidai.

A wata tattaunawa da  aka yi  da  tsohon sarkin ya ce  tun kafin shigowar  annobar Korona, ya kamata gwamnati ta dauki wadannan matakai.

A hirar da aka yi  da shi a gidan talabijin din Arise TV a ranar Juma’a, 4 ga watan Satumba, Sanusi  ya ce cire tallafin man fetur da aka yi, shi ne abin da ya dace.

Ya kara da cewa“Wadansu matakai da ake dauka kwanan nan, wadanda aka aro daga IMF na cire tallafin man fetur, duk da akwai zafin yin hakan, su ne abubuwan da su ka dace a yi idan ana so kudin asusun gwamnati su karu.

Sai dai duk da nuna goyon baya da tsohon gwamnan na CBN ya yi na zaftare tallafin mai, ya ce akwai gyara a lamarin yadda kasar ta ke kashe kudi.

“Gwamnati ta duba yadda ta ke kashe kudi, ta tabbatar cewa yana kai wa ga talakawan kasa.”

A cewarsa, ya kamata gwamnatin tarayya ta rika kashe kudi ne a harkar ilmi, ruwan sha, cigaban karkara, ya ce wannan ya fi muhimmanci a kan gina gidaje da gada.

Tsohon sarkin Kano ba kasafai yake fitowa da ra’ayinsa ya dace da goyon bayan mutanen kasa ba musamman talakawa, wannan ma ya ci karo mafi rinjayen mutanen kasa da ke ganin ba a wannan lokaci ne ya dace a kara yawan kudin ba, hasalima kamata ya yi a fito da wasu hanyoyin saukakawa talaka matsin rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *