Spread the love

A ranar Laraba data gabata watan Satumban 2020 ne ƙungiyar masu gidajen mai masuzaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta umarci ‘ya’yanta su ƙara kuɗin farashin man fetur zuwa Naira 162 kan kowace lita, amma wasu sun ce za su sayar 158 wasu 160.

Ipman ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon karin kudin mai dagwamantin Najeriya ta yi zuwa N151.56k.

Wannan ne karo na uku da gwamnati take sauya farashin mai a ‘yan watannin baya-bayan nan, sai dai sabanin wasu lokutan da ake rage farashin, karin na man na wannan karon shi ne mafi yawa a baya-bayan nan cikin gwamnatin Buhari.

Tun bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari karagar mulkin Najeriya, an yi tasamun ƙarin kudin man fetur a lokutan daban-dana, kamar dai yadda ya sha faruwa a gwamnatocin baya.

Duk da cewa ba wannan ne karo na farko da aka taɓa yin ƙarin farashin mai aƙasar ba, hakan ya tayar da hankalin mutane da dama.

BBC ta yi nazari kan tarihin ƙarin farashin mai da shugabannin da suka gabatasuka sha yi a ƙasar, tun daga 1973 lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon zuwayau.

 Janar Yakubu Gowon ne shugaban kasa na farko da ya fara kara farashinman feturA 1973, Janar Yakubu Gowon ya ƙara farashin man fetur wanda a iya cewa shine na farko, daga kobo shida zuwa kobo takwas da rabi, wato kashi 40.8 cikin 100 kenan a kan kowace lita.

A 1976, Janar Murtala Muhammad ya ƙara farashin man daga kobo takwas darabi zuwa kobo tara, wato da kashi 0.59% kan kowace lita.

Farashin fetur: Sauyin da aka samu a Najeriya cikin shekara 20

‘Man fetur ɗin da Najeriya ke sayowa na da guba’Ranar 1 ga watan Oktobar 1978 ne Janar Olusegun Obasanjo ya ƙara farashindaga kobo tara zuwa kobo 15.3, wato kashi 70 cikin 100 kan kowace lita.

20 ga watan Afrilun 1982, Alhaji Shehu Shagari ya sake ƙara farashin daga kobo15.2 zuwa kobo 20, wato kashi 30.71 cikin 100, a kan lita guda.

A ranar 31 ga watan Maris na 1986 kuma Janar Ibrahim Babangida ya sake ƙarafarashin daga kobo 20 zuwa kobo 39.5, kashi 97.5 cikin 100 kan kowace lita.

Janar Babangida ya sake ƙara farashin a ranar 10 ga watan Afrilun 1988, dagakobo 39.5 zuwa kobo 42, kashi 6.33 kenan cikin 100 kan kowace lita.

A ranar 1 ga watan Janairun 1989, Janar Babangida ya sake ƙara farashin dagakobo 42 zuwa kobo 60 ga motocin da ba na gwamnati ba.

Ranar 19 ga watan Disambar 1989 ya mayar da farashin na kowa da kowa.Janar Babangida ya sake ƙara farashin daga kobo 60 zuwa kobo 70 a ranar 6 gawatan Maris 1991. Wannan ƙari ya zamo da kashi 16.67 cikin 100.

Shugaban riƙon ƙwarya Chif Ernest Shonekan shi ma ya yi wannan ƙarin farashiranar 8 ga watan Nuwambar 1993, daga kobo 70 zuwa naira biyar, ƙarin da yazama da kashi 614%.

Shugabannin kasar Najeriya da suka kara farashin man fetur a lokutanmulkinsu

A ranar 22 ga watan Nuwambar 1993 ne Janar Sani Abacha ya rage farashinman daga naira biyar zuwa naira uku da kobo 25, ragin kashi 35 cikin 100 kenankan kowace lita.

Ranar 2 ga watan Oktobar 1994 kuma Janar Abachan ya ƙara farashin daganaira uku da kobo 25 zuwa naira 15, ƙarin kashi 361.54%.

A ranar 4 ga watan Oktobar 1994 Abacha ya sake rage farashin man daga naira15 zuwa naira 11, ragin kashi 26.67%.

Shi ma Janar AbdusSalam Abubakar ya ƙara farashin daga naira 11 zuwa naira25, ƙarin kashi 127.27%, a ranar 20 ga watan Disambar 1998.

A watan Janairun 1999 kuma ya rage farashin daga naira 25 zuwa naira 20.Cif Olusegun Obasanjo ya ƙara farashin man daga naira 20 zuwa naira 30 aranar 1 ga watan Yunin 2000.

A ranar 8 ga watan Yunin 2000 Obasanjo ya rage farashin daga naira 30 zuwanaira 22, ragin kashi 10 cikin 100.

Obasanjo ya sake ƙara farashin daga naira 22 zuwa naira 26 ranar 1 ga watanJanairun 2002.

Cif Olusegun Obasanjo ya kara farashin mai kusan sau biyar a zamaninmulkinsa

A watan Yuni 2003 Obasanjo ya sake ƙara farashin daga naira 26 zuwa naira 42.Ranar 29 ga watan Mayun 2004 kuma chif Obasanjo ya mayar da farashin mannaira 50. Ƙarin kashi 19.05%.

Ranar 25 ga watan Agustan 2004 ya sake ƙara farashin zuwa naira 65.Ƙarin farashin mai na ƙarshe da Obasanjo ya yi shi ne ranar 27 ga watan Mayun2007, inda man ya koma naira 75, ƙarin kashi 15.38%.

Shugaba Umaru Musa ‘Yar aduwa ya rage farashin mai daga naira 75 zuwa 65 awatan Yunin 2007.

Umaru ‘Yar Aduwa ne kadai wanda bai ƙara farashin man fetur ba cikinshugabannin da suka mulki Najeriya tun daga 1973.

A ranar 1 ga watan Janairun 2012 Goodluck Jonathan ya yi ƙoƙarin ƙara farashinzuwa tsakanin naira 138 da naira 250, amma daga bisani ya tsaya a kan naira97.

An yi zanga-zangar nuna adawa da janye tallafin da Jonathan ya so yiA watan Janairun 2015 kuma Shugaba Jonathan ya rage farashin daga naira 97zuwa naira 87.

Ƙarin farashin mai a mulkin Buhari

Karin farashin mai na farko da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi shine ba da damar sayar da man a kan naira 87 da kobo 50 a gidan man ‘yankasuwa ko da yake farashin bai sauya ba a gidajen man NNPC.

Tun daga wannan lokaci ba a sake samun ƙarin farashin man ba sai a ranarLaraba 11 ga watan Mayun 2016 da gwamnatin Shugaba Buhari ta mayar da shinaira 145.

A watan Maris 2020 – faɗuwar darajar fetur a kasuwar duniya ta sake tilastawagwamnatin rage kudin man daga N145 zuwa N125.

Bayan wata guda, a karo na biyu a watan Mayun 2020, hukumar ƙayyade firashinalbarkatun man fetur ta PPPRA ta sanar da sabon farashi daga N121.50 zuwaN123.50 lita guda.

Sai kuma a ranar Laraba 2 ga watan Satumban 2020 da ƙungiyar masu gidajenmai masu zaman kansu ta Najeriya IPMAN, ta umarci ‘ya’yanta su ƙara kuɗinfarashin mai zuwa Naira 162 kan kowace lita.

Karin ya biyo bayan sanarwar da hukumomin Najeriya suka yi na kara kudin maizuwa N151.56k.

Dogaro da man fetur – Sharhi da aka yi a 2016

Najeriya ƙasa ce da Allah ya albarkace ta da arziƙin man fetur, wanda kuma dashi ne ta dogara wajen samun kuɗin shigarta.

Sai dai duk da irin wannan ɗumbin arziƙin mai da Najeriya ke da shi, bai saƙasar ta wadatar da al’ummarta da man ba, ta yadda hakan ke jefa mutane cikinhalin ƙa-ƙa-ni-ka-yi a lokuta da dama.

Za a iya danganta hakan da rashin ingantattun matatun mai da ƙasar ba ta dasu, ta yadda sai dai bayan ta sayar da ɗanyen manta ga wasu ƙasashen duniya,sai kuma ta koma wajensu ta sayo tattaccen man da za a yi amfani da shi.

Hakan ya sa take sayo man da tsada, dalilin da ya sa gwamnati biyan tallafinrarar man fetur ta yadda ‘yan ƙasa ba za su saya da tsada sosai ba.

Gwamnatin baya ta Goodluck Jonathan ta yi yunƙurin janye tallafin man, ammasai aka dinga zanga-zangar nuna adawa da wannan mataki.

Hangen masana tattalin arziki kan janye tallafin man fetur a 2016Masana tattalin arziƙi sun yi ammanar cewa janye tallafin man fetur na daamfani da kuma rashinsa. Sai dai da yawa sun ce amfaninsa na dogon zangone.

Masanan sun ce a halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki a yanzu, gwamnati bata da kuɗaɗen da za ta tallafa wajen biyan rarar.

Haka kuma ana iya amfani da makuɗan kuɗaɗen da ake kashewa wajenbiyan tallafi a yi wasu ayyukan raya ƙasa da suke da muhimmanci sosai.Za a samu gasa tsakanin manyan ‘yan kasuwa inda za su dinga karyar dafarashin man, domin tsoron kada wani ya fi su samun tagomashi a harkar,kamar dai irin abin da ya faru a ɓangaren kamfanonin sadarwa.

Akwai hasashen cewa man zai wadata sosai a ko ina da kuma tabbacin dainasamun dogayen layuka a gidajen mai.

Duba da halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki a yanzu da irin wahalhalun damutane ke fuskanta, wasu na ganin janye tallafin man ba zai yi wa al’ummadaɗi ba, musamman talakawa.

Farashin kuɗin abin hawa da na kayan masarufi zai ƙara hawa.Zai bai wa ‘yan kasuwar man damar sanya farashi son ransu, ta yadda manzai fi farashin da gwamnati ta ƙayyade tsada.

Fatar da mutanen kasa suke da ita wannan karin ya zama sanadin farfadowa da tattalin arziki abin da zai sa a rage kudin man sosai fiye da yanda ake zato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *