Spread the love

Wasu ‘ya‘yan kungiyoyi matasa masu zaman kansu a jihar Osun sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadin karin farashin kudin wuta da man fetur da gwamnatin Buhari ta yimin.

A ranar Juma’a, 4 ga watan Satumba, 2020, aka wayi gari a babban birnin Osogbo na jihar Osun da zanga-zanga ta dalilin karin da gwamnatin tarayya ta yi wanda ba su gamsu da hakan ba.

A cikin makon nan ne aka kara farashin shan wutan lantarki, bayan haka farashin litar man fetur ya kara kudi zuwa N160 a wasu gidajen man kasar.

Jaridar Punch ta ce masu nuna rashin goyon bayan wannan mataki da gwamnati ta dauko sun faro zanga-zangar lumanarsu ne daga Freedom Park na Osogbo, rahoton ya bayyana cewa an fara wannan zanga-zanga ne da kimanin karfe 8:30 na safen yau.

Masu zanga-zangar su na dauke da allunan da ke nuna fushinsu karara a kan karin kudin wutan lantarki da kuma kudin man fetur in da suka yi tir da lamarin.

Wasu daga cikin masu wannan zanga-zanga sun koka da cewa karin kudin wuta da mai da aka yi, ya fito da rashin tausayin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wadda talaka ya zaba.

Zuwa lokacin da mu ka samu wannan rahoto, ana gabatar da zanga-zangar cikin kwanciyar hankali ba tare da an samu wani tashin hankali ba.

A Nijeriya yajin aiki da zanga-zanga ne ake ganin gwamnatoci na fahimta shi ne ya sanya ake yinsu duk sanda ba a gamsu da hukuncin gwmnati ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *