Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yabawa Gwamnan jihar Bauchi Dakta Bala Muhammad (Kauran Bauchi)  bisa kokari da ya yi akan aikin gina masallacin da kuma manyan ayyuka da yake gudanarwa a jihar Bauchi ba tare da nuna bangaranci ba.

Gwamnan a jawabinsa ya nuna farincikinsa yanda kungiyar ke karantar da mutane lungu da sakon kasar Nijeriya, ya yi fatar su daure da aikin.


Ya ce gwamnatinsa a shirye take ta cigaba da taimakawa addinin musulunci a jihar Bauchi.


Taron bude masallacin ya samu halartar manyan Malamai daga sasssa daban- daban na kasar nan da suka hada da Sheikh Yusif Sambo Rigachikun, Sheikh Sa’id Hassan Jingir, Sheikh Nasir Abdulmuhyi, Sheikh Abubakar Salihu Zariya da sauran manyan Malamai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *