Spread the love


Daga Aminu Abdullahi Gusau.

A yau ne fadar gwamnatin jihar Zamfara a karkashin jagorancin gwamna Bello Muhammed Matawalle ta karbi ba kuncin Hafeez Ibrahim Ibrahim, kuma ta hannunta shi ga Iyalansa.

Shi dai Hafeez Ibrahim Ibrahim, dan jihar Zamfara ne, wanda Jami’an tsaro na kasar Saudiyya suka tsare fiye da shekara ukku, domin zargin ya saka haramtaccin kaya a jikarsa, ana tsare da shi tun shekarar 2016, amma gwamnatin data gabata ta kasa yin wani abi game da wannan bawan Allah.

Da yake jawabi, kafin hannun tashi ga yan uwansa, Gwamna Matawalle yace jami’an tsaro na Saudiyya sun tsare Ibrahim ne bisa zargin yana safarar miyagun kwayoyi, inda yace wasu ne suka zalunce shi suka saka masa kayan a jikarsa, lokacin da suke tafiya Kasar ta Saudiyya.

Daga nan gwamnan ya ce “Alhamdulillah, yau Hafeez Ibrahim Ibrahim ya hadu da ‘yan uwansa bisa ga jajircewar wannan gwmnati tamu na ganin cewa ko yaushe mutanen zamfara su ne a gabanmu, kuma ba zamu kasa a gwiwa ba damu kwato masu ‘yancinsu.”

Ya kara da cewa, daga karshe dai bayan mun yi ta gwagwar maya, ganin an sako shi, daga karshe dai gwamnatin ta Saudiyya ta wanke Ibrahim Ibrahim bisa ga zargin da ake yi mashi.

Daga karshe gwamnan yaja kunnen matafiya Kasar ta Saudiyya da suyi hankali kuma su kula da kayan su idan domin kaucewa irin abinda ya faru ga Hafeez Ibrahim Ibrahim.

Gwamna Bello Muhammed, yayi godiya ta musamman ga gwamnatin Kasar Saudiya da kuma gwamnatin Najeriya, bisa ga kokarin da sukayi na ganin an sako wannan bawan Allah.

Da yake bayani na godiya, Malamin ya godewa duk wayanda sukayi kokarin ganin an sakoshi ciki da wajen wannan kasar, hakan abin yabawa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *