Spread the love

‘Yar wasan kwaikwayo a masana’antar shirya finafinnan Hausa da ake kira Kannywood Aisha Aliyu Tsamiya masu kallon finafinnan Hausa suna mutunta kan kamun kan da suke ganin tana da shi a cikin abokan sana’arta mata.

Aisha Tsamiya a duk sanda ta fito a wasan kwaikwayo an fahimci ba a ganinta da shigar bayyana tsiraici kuma ba ta hawan rol da za ta fadi kalmomin batsa ko nuna rashin kunya a tsakaninta da aboki ko abokiyar wasan.

Masoyanta sun yi ta fatan gwanar ta su ta yi aure don tun a lokacin da ta shigo masana’antar suke ganin ba ta dace da harkar ba.

Aisha ba ta cika damuwa da harkokin kafofin sada zumunta(soshiyal media) ba, hasalima ba ta yi fice wajen tara yawan mutane, da neman kudi a kafofin ba, kwatsam sai aka ga ta wallafa wasu hotunanta a turakarta ta Instagram abin da ya jawo hankalin mutane da tambayar ko Aisha na son ta shiga harkar bayar da bayani da nuna wanka kamar yadda abokan sana’arta ke yi.

Aisha Tsamiya

Managarciya ta fahimci yanda masu kallon fim na hausa ke girmama Aisha saboda kama kanta da ta yi kan haka yakamata ta rike girman da suke gani nata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *