Spread the love

Daga Bashir Abubakar Jega.

Injiniya Junaid Jandutsi dake Karamar Hukuma Jega Jihar Kebbi ya samu fasahar kera babura da motoci da samfur na jirgi wasu kalan kayan amfani.

Shugaban Karamar Hukumar Jega kana ya yaba da kwazon Injiniya Jandutsi ya kuma lashi takobin daukar matakin karfafa masa guiwa domin ganin al’umma ta ribantu da fasahar wannan injiniyan.

A Nijeriya ana samun yara masu kaifin basira da suke iya harkar kere-kere da za su samu gudunmuwar tallafin gwamnati ko ‘yan kasuwa lamarin basirarsu zai amfani kasa da al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *