Jagororin sun yi ta kokarin boye wannan bambanci tun kafin bayyanar lamarin a gaban magoya bayansu a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar da aka gudanar a gidan gwamnati a ranar Litinin data gabata.

Managarciya ta samu labarin Bafarawa ya amayar da duk abin da ke damunsa a tafiyar da jam’iya kamar yadda shi ma Gwamna Tambuwal ya yi hakan a gaban masu ruwa da tsaki na jam’iyar a Sakkwato.

 “jagororinmu a jiha(Tambuwal da Bafarwa) kawunansu ya rabu, lalle jagororin cikin bayanansu an samu matsaloli amma mun so a fito da wani tsari wanda yakamata shugabannin su yi tun farko, kasan wanda yake babba koyaushe tunaninsa daban ne dana dan karami don ba ruwansa da wahala, mun so a kasa mukaman nan bangaren wane da wane.

“Sai gashi kawai aka ce an kafa kwamiti a kananan hukumomi  su je su yi aiki mun yarda su yi aiki amma a gyara kwamitin domin ‘yan bagare biyu ne kawai aka sanya don ba mu son a samu matsala, maganar kashi ba ta taso ba, tsohon labari ne ba mu aminta da shi ba don mu muka zabi gwamnati, a lokacin da za ka yi mana maganar kaso a lokacin da gwamna ya zo da mutanensa ba mu zabe sa ba, a yanzu ko mun kada masa kuri’a  kamar kowa a jam’iya daya muke sai dai mu yi kaso a raba daidai(50-50) tun da mun yi aiki.

“Mu bangaren Bafarawa muke shi ne jagoranmu duk abin da muka samu albarkacinsa ne dole mu yi masa da’a duk sanda abin bacin rai ya same shi dole ranmu ya baci, in najin dadi ne dole haka, kai kasan ba a cewa Garkuwa bai iya wani abu a Sakkwato ba gaskiya ba ne, duk wanda yake  Sakkwato yasan yanda aka yi zaben gwamna na gaba daya dana cike gurbi(inconclusive) ko sanda Garkuwa yake gwamna bai sha wahala kamar lokacin zaben ba.” A bayanan da  Managarciya ta samu ga wata majiya.

Abdullahi Yusuf Hausawa mamba ne a kwamitin rikon kwarya na jam’iyar PDP a Sakkwato ya ce a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar an tsara kowace karamar hukuma za su zauna kowane bangare nada wakilci sai su fito da mutanen da za su jagorance su jam’iya za ta sanya ido yadda abubuwa za su tafiya, PDP daya ce ba zance abaiwa wani kaso.

Ya ce bai san wani wuri a tsarin dokar jam’iya da ya hana shugaban jam’iya na jiha  ya fito wuri daya da Gwamnan jiha ba. Kamar yadda wasu ke ganin kundin ya hana haka.

Zaben da za a gudanar a Assabar 5 ga Satumba mai zuwa na kananan hukumomi da wanda za a gudanar 12 ga watan na shugabannin jam’iya na jiha ya sanya baraka a jam’iyar a matakin jiha abin da wasu ke ganin dimukuradiyya ta gadi haka kuma za a silhunta a tafi tare domin dukansu suna da manufa daya ita ce cigaban  jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *