Spread the love

Muhammad M. Nasir

Jam’iyar PDP a jihar Sakkwato ta sanya ranar zaben shugabaninta da za su tafiyar da jam’iyar shekarru hudu masu zuwa.

A bayanin da daya daga cikin mambobin kwamitin rikon kwarya na jam’iyar a jihar Sakkwato Abdullahi Yusuf Hausawa ya sanar da Managarciya ya ce za a yi zaben shugabannin kananan hukumomi 23 a ranar Assabar 5 ga watan Satumba na shekarar 2020.

Idan sati ya zagayo Assabar 12 ga wata a yi zaben shugabannin jam’iya a matakin jiha.

Wasu na ganin kamar jam’iyar a jihar Sakkwato na fama da rikicin cikin gida da ba’a son al’umma su san da shi  hakan ya sa aka yi ta daga lokacin zaben kafin sanya wannan ranar.

Wasu bayanai da ba a tabbatar da su ba, sun ce tsohon gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ne ya kokawa uwar jam’iyar kan bai gamsu da yadda zaben shugabannin mazabu ya gudana ba  domin an janye magoya bayansa a maye su dana gwamna Tambuwal a mafiyawan mazabun jihar Sakkwato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *