Spread the love

 Fargaba ta mamaye jihar Kogi kan hukuncin da kotun koli za ta yanke a gobe Litinin game da karar da aka sanya gwamnan jihar Kogi na zargin an yi magudi da arinizo a zabensa na gwamna da aka yi a kwanakin da suka gabata.

Kotun kolin ana sa ran za ta yanke hukunci ne kan daukaka kara guda biyu da aka yi gabanta na kalubalantar Gwamna Yahaya Bello a zabensa karo na biyu da hukumar zabe ta gamsu da shi.

Dan takarar jam’iyar PDP Injiniya Musa Wada da ‘yar takarar gwamna a jam’iyar SDP Natasha Akpoti ne suke kalubalantar zaben a kotun koli.

A gobe ne dukan mutanen uku za su san matsayarsu kan wannan shari’a ta zaben gwamnan jihar Kogi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *