Spread the love

 

 Masu karbar fansho a kananan hukumomin jihar Sakkwato sun koka kan kin sanya su a tsarin biyan mafi karancin albashi a tsawon lokaci da gwamnatin jihar Sakkwato ta yi.

Masu karbar Fanshon sun bayyana cewa  ba’a yi masu adalci ba a bambanta su da takwarorinsu ma’aikatan gwamnati na jiha da tazara mai yawan gaske wajen  biyansu hakkokinsu, ba su ci gajiyar karin da aka yi ba tun ana biyan mafi karanci albashi 18,000 har ya koma 30,000, biyan fansho da ake yi masu bai canja ba.

A wasu takardun koke guda biyu da shugabannin hadaddiyar kungiyar fansho na ma’aikatan kananan hukumomi da ma’aikatan ilmi dana lafiya suka aikawa majalisar dokokin jihar Sakkwato domin ta sanya baki ga wannan matsalar da suka yi ta biya hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

A bayanin  sun ce ma’aikatan kananan hukumomi da ilmi da lafiya bayan sun kammala aikinsu a tsawon shekara 35, a tsarin sabon albashi na 18,000 da suka karba tsawon shekara uku, babu wannan tsarin na kari a Fanshon kananan hukumomin jihar Sakkwato, balle har su yi tsammanin sabon da aka yi su shiga ciki.   

“Duk tsarin albashi shi ne tsarin biyan Fansho, takwarorinmu da ke aiki a matakin jiha an sanya masu wannan tsarin ana biyansu da mafi karancin albashi da aka amince da shi.

“Gaskiyar magana a misali wanda ya yi ritaya ma’aikaci ko malami a mataki na 14 karamin mataki na 4 Fanshonsa a wata dubu 32,923:52, garatitu kuma zai kasance miliyan 1,481,558:40, Kamata ya yi fanshonsa ya zama dubu 54, 456:00, garatitu kuma miliyan 2,450,520. Ma’aikacin lafiya shima da ya bar aiki a wannan matakin yana karbar 40,200:00 fanshonsa na wata, garatitunsa miliyan 1,700,000:00, Amma in za a biya shi yanda ya dace Fanshonsa zai zama dubu 220, 000:00   garatitu(CONHENSS)  miliyan 9, 700,000:00. Kan haka muke rokonka(Kakakin majalisa) ka taimaka mana a tabbatar da an rika biyan mu hakkinmu kamar yadda dokar aikin gwamnati  ta tanadar ga wadan da suka yi ritaya.”  a cewar bayanin.

Kungiyar ta sake tura takardar neman sanin matsayar da majalisa ta cimma kan kokensu a ranar 6 ga Junairu 2020, domin masu karbar fanso da al’ummar jihar Sakkwato su san in da aka kwana sannan su san wace matsaya za su dauka  a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *