Jarumi Adam A Zango ya ziyarci ofishin hukumar tace finai finai reshen jihar Kano, inda jarumi kuma mawaki Adam A Zango ya Kaiwa shugaban kungiyar Ismail Na’abba Afakallah ziyarar ban girma tare yin mubaya’a ga shugabancin nashi.

Jarumin ya jima yana takon saka da hukumar in da ya hana shi shiga Kano yin aikin fim da yi masa barazanar in ya kuskura ya shigo za ta kama shi da daure shi.

A lokacin Zango ya firgita don bai shiga Kanon ba sai dai ya yi ta kalamai na nuna shi ne kawai hukumar ba ta so ko bayan furuncinsa na ya fita daga kungiyar ‘yan Wasa ta Kano waton Kannywood.

Kwatsam sai ga hoto Jarumin ya kai ziyarar ban girma a hukumar da ya ki was biyayya a baya Wanda za a Kira haka da ya yi amai ya lashe.

Zango bai fadi dalilin daukar matakin ba sai dai ya ce ya koma Kan aikinsa a Kano Kan haka Managarciya na yi masa fatan alheri ga wannan hukuncin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *