Spread the love

Daga Muhammad Nasir.

“Anan Sakkwato da PDP ke mulkinmu  ba wani cigaba, mulki ne na mutum daya Tambuwal shi kadai ne ke yin abin da ya ga dama ban yi tsammanin akwai wani mutum da ke ba shi shawara ba duk da ya debi mutane da yawa matsayin masu bayar da shawara amma ba su da amfani, ko ba su bayar da shawarar ko ba ya dauka tun da ba wani abu da aka tsinanawa talaka a Sakkwato. 

“Dubi harkar ilmin wadda ita ce kashin bayan kowane cigaba, matasanmu da suka kare jarabawar kammala makarantar sikandare a shekarar data gabata shekara daya kenan ba a biya masu kudin jarabawa ba, gwamnati ta ki biya, makarantunmu dake birane ba su da wurin zama balle na kauye, jami’a mallakar jiha na bukatar daukin gaggawa, jarabawar share fagen shiga jami’a da yaranmu suka yi ba a biya ba.

 “Tun da shi gwamna lauya ne bai taba aikin gwamnati ba, daga dan majalisa ya zama gwamna da masu bayar da shawara sun san aikinsu da ba su bari ilmi ya lalace haka tun da kowa ya san gwamnati ke daukar ilmi.”

Batista Abubakar Aliyu Sanyinna jigo ne a jam’iyar APC a jihar Sakkwato Kuma tsohon Dan takarar gwamna a APC, kwamishinan yada labarai ne a gwamnatin Wamakko ya furta hakan a zantawarsa da manema labarai a satin da ya gabata ya ce  gwamna na cin karensa ba babbaka. Allah ya gwada masu abinsu sun yi zalunci kuma ya fara cinsu. 

Ya ce Allah ya san suna iya karawa da gwamnatin Sakkwato ko da ta maza ce balle suna kallonta ta koma ta ‘yan mata “mu muna son a yiwa mutanen Sakkwato adalci gwamnati ba ruwanta da ceton al’umma tun da suka zalunce mu ba su sake ganin daidai da ikon Allah.” A cewar Sanyinna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *