Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Kamfanin Alfijir Bread dake Gusau babban birnin jihar Zamfara ya ce karin da aka samu ga farashin biredi, anyi shi ne ba da manufar matsar da masu sayen biredin ba.

Sakataren Kamfanin na Alfijir Bread, Alhaji Habibu Alfijir ne ya yi wannan bayani Lahadi data gabata yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishin sa dake garin Gusau.

Ya ce, babban dalilin da yasa haka shi ne, hauhawar farashin kayan da ake yin biredin da su, kuma sun yi iya kokarinsu, domin kaucewa karin kudin amma abin ya cutura.

Sakataren ya kara da cewa fulawa, suga, kwai, yis, madara, bota da dai sauran abubuwan da suke hadi wajen sana’ar ta su duk sunyi tashin gwabron zabo.

Alhaji Habibu Alfijir a don haka ya ce ya zama wajibi su kara farashin biredi, in har suna son su ci gaba da wannan sana’ar, ya kara da cewa Kamfanin fulawa na yi masu karin kudin fulawa yadda suka ga dama, kuma ba yanda za su yi.

“Kafin mu yi karin farashin biredi sai da muka yi kokarin mu hadu da mai girma gwamna Bello Muhammed Matawalle, domin mu fada masa halin da muke ciki, amma hakan bai samu ba domin an gaya muna yayi tafiya.

“Hakikanin gaskiya munso mu ganshi domin mu yaba mashi bisa namijin kokarin da yayi na samar da tsaro a wannan jihar, domin yanzu muna kai biredin mu lungu da sako na wannan jihar ba tare da wata fargaba ba, mu sayar kuma mu dawo lafiya, ba kamar shekarun baya ba. Inji shi.

Daga karshe ya sheda cewa bayan sun kammala taro da kungiyar masu sayar da shayi, sun yanke shawarar kara naira dari, misali biredin da ake sayarwa naira dari ukku, yanzu zai koma dari hudu, na dari biyu da hamsin zai koma dari ukku da hamsin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *