Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Kungiyar lauyoyi musulmai reshen jihar Sakkwato bayan dogon nazari da fahimtar yadda lamari ke tafiya sun yanke shawarar ba za su halarci taron kungiyar lauyoyi ta kasa NBA kan janye takardar gayyatar halartar taronsu karo na 60  da suka yi masa.

Reshen kungiyar ya fitar da bayani ga manema labarai wanda shugabanta Muhammad Buhari Abubakar da Sakatarensa Muhammad Mansur Aliyu suka sanyawa hannu sun yi tir da janye gayyatar kan zargin sabawa doka da kin bin doka da oda ga Gwamnan Nasir Elrufa’i.

Kungiyar MULAN ta umarci mambobinta a jihar Sakkwato kar su halarci taron su kauracewa lamarin kwata-kwata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *