Kungiyar lauyoyi musulmai(MULAN) reshen jihar Kaduna ta yi matsayar ba za ta halarci taron kasa na kungiyar lauyoyi(NBA) ba, wanda aka shirya gudanarwa a yanar gizo kan rikita-rikitar da ta taso ta janye gayyatar halartar taron da aka yi wa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufa’i wanda shi ne bako mai jawabi a wurin bukin.

Taron wanda suke yi duk shekara a wannan shekarar kungiyar ta rabu gida biyu kan janye katin gayyatar Malam Nasir don ya sanyawa taron albarka domin suna ganin ba ya girmama hakkin dan adam a tsawon lokaci wanda bai kamata irinsa ya tsaya gaban lauyoyi yana kora masu jawabi ba.

Mataimakin shugaban kungiyar lauyoyi musulmai Abbas Masanawa ya nuna wannan abun bai da ce ba su ba su gamsu da hakan ba matukar ba a sake gayyatar El-rufa’i ba mambobinsu 500 ba za su halarci taron ba.

Majalisar shari’a ta kasa ita ma ta ga laifin NBA kan janye gayyatar sun ce ai yakamata a saurari Elrufa’i a taron.

Managarciya na kallon wannan janyewar na tattare da harkar addini da kabilanci wanda ya yi katutu a Nijeriya.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *