Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir.

Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a yau Assabar a dakin karatu na Obasanjo dake Abeokuta jihar Ogun.

Da yawan mutane na daganta wannan ziyara nada nasaba da kudirin da ake ganin gwamnan yana da shi na neman tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Tambuwal ya dade da kudirin son ya mulki Nijeriya tun bayan da ya dare saman kujerar kakakin majalisar wakillan Nijeriya wadda ita ce kujera ta hudu a tsarin mulkin kasar Nijeriya.

Ya so ya tsaya takarar shugaban kasa a Shekarar 2015 abin bai yiwu ba, ya yi takarar gwamnan Sakkwato ya samu nasara, a 2019 ya shiga zaben fitar da gwani na jam’iyar PDP abin da bai yi nasara ba, sai ya sake dawowa neman a sake zabarsa gwaman a karo na biyu abin da yay i nasara a zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *