Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Mai baiwa gwamnan Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal shawara kan harkokin jinkai da kiyaye hakkin dan adam Hajiya Ubaida Muhammad Bello ta ce sun samu labarin kawun  Salisu Muhammad mai shekara 45 ya tsare shi  tsawon shekara 15 a garin Gidan Madi cikin karamar hukumar Tangaza dake jihar Sakkwato ta hannun makwabtansu dake tunanin ma kila mutumin ya rasu.

Ubaida ta ce sun yi tsamanin mutumin ba ya raye don sun yi sama da shekarru 10 ba su ganshi ba.

“Mun same shi cikin mawuyacin hali fitsari da komai nan yake yi ba wata kulawa da yake samu.” A cewarta.

‘Yan sanda a jihar ne suka kubutar da shi, mai magana da yawun rundunar ta jihar Sakkwato ASP Muhammad Sadik ya tabbatar da faruwar lamarin kuma bincike ya nuna mutumin nada tabin hankali.   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *