Spread the love

Gidauniyar Sa’ar mata wadda ke tallafawa matasa da marasa galihu a jihar Sakkwato ta yi bukin yaye mata da aka koyar da su sana’o’in hannu daban daban wadan da aka zabo a kananan hukumomin Bodinga da Dange Shuni da Tureta,  tare da baiwa matasa 50 takardun cikewa na share fagen shiga jami’a(JAMB).

A wurin bukin da aka gudanar a harabar ofishin Gidauniyar dake unguwar Runjin Sambo wadda ta kafa  gidauniyar Barista Sa’adatu Yunusa Muhammad ta ce sun himmatu wajen karfafawa matasa a jihar Sakkwato musamman don cimma muradunsu na zama masu amfani a cikin al’umma.

Barista ta ce matasanmu na bukatar taimako a haujin karatu da samar musu abin dogaro da kai ba za mu yi kasa a guiwa ba da irin abin da Allah ya hore mana za mu bayar da tamu gudunmuwa ga gina al’umma musamman matasan jihar nan maza da mata.

Ta ce makamancin shirin na kan gudana amma ba da sunan gidauniyar ba, don haka ta yi kira ga wadan da suka amfana da shirin su yi aiki tukuru a wurin amfani da ilmin da suka samu domin amfanar da jihar Sakkwato.

Gidauniyar Sa’ar mata ita ce irinta ta farko a jihar Sakkwato da mace ta assasa da zimmar koyar da sana’o’i  ga mata da ragewa matasa maza wahalar karatu.

“Matasanmu na son karatu ba hali ne, yakamata masu hali a cikin al’umma su fitar da dukiyarsu su rika taimako musamman ‘yan siyasa su rika yin abin da zai taimaki jama’arsu, su gina su ba wai a rika rushe su ba, duk wanda ya gina matasa ya gina al’umma, ba da gudunmuwa ga gina al’umma mun fara kenan har karshen rayuwarmu burinmu dai jama’a su samu tudun dafawa.” A cewar Barista Sa’adatu.

Barista Sa’adatu Yanusa wadda ta assasa Gidauniyar SA’AR MATA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *