Spread the love

Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya aiyana Juma’a ta zama ranar hutu ga ma’aikatan jihar Sakkwato domin bukin murnar shigowar sabuwar shekarar musulunci.

Gwamna Tambuwal ya bayar da hutun ne bayan majalisar sarkin musulmi ta sanar da cewa Juma’a ne yake 1 ga watan Muharam na shekarar 1442, domin ba a samu labarin ganin wata na hakan ya sanya Zulhajj ya cika kwana 30.

Gwamnan ya taya dukkan al’ummar musulmi murnar farawar sabuwar shekara da  fatan samun kariyar Allah da albarkarsa.

A  bayani da shugaban ma’aikata Sani Garba Shuni ya sanyawa hannu  gwamnan ya nemi mutanen jihar Sakkwato su ci gaba da yin addu’ar samun zaman lafiya da cigaban jiha da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *