Spread the love

Jaridar daily trust ta gano cewa manoma da masunta dake cikin al’ummar arewacin jihar Borno ba a barinsu su tafi gona ko wurin kamun kifi sai sun biya haraji ga mayakan.

Kananan hukumomin dake arewacin Borno sun hada da Abadam da Guzamala da Magumeri da Gubio da Kaga da Kukawa da Marte da Mobbar da Monguno da Nganzai.

Mutanen suna biyan kudi kafin ka tafi gonarka ya danganta da girman gona Wanda yaki biya Kuma za su kashe shi.

A wadan nan wurare ya nuna akwai in da Boko Haram ke rike da shi ta la’akari da yadda majiyoyin da daily trust ta samu suka fadi Wanda Mujallar Managarciya ta ci karo da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *