Spread the love

Boko Haram bangaren ISWAB a ranar Talata ne akalla sun kashe soja takwas sun raunata uku a lokacin da suka yi masu kwantan bauna a garin Kukawa a gefen arewacin jihar Borno.

Sojojin sun shirya ne za su je garin don su kawar da mayakan da aiyukkansu suka yawaita a garin anan suka Yi masu bazata don suna da labarin motsin sojojin.

A tawagar akwai manyan jami’an soji biyu da sauran sojoji 28, Boko Haram sun kashe 8 daga cikinsu uku suka samu rauni, biyu suka bace daga baya an gane su.

Haka ma sama da kwana goma da suka wuce sun ce dimbin jama’a a garin da suka hada da matasa maza da mata.

Ranar litinin sun kone babbar asibiti dake garin Magumeri sun kashe wata uwa maishayarwa suka sace maganin dake cikin asibitin da wasu kaya masu amfani kafin su kone ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *