Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da sace mutun hudu a gidan tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Alhaji Muhammed Dankande Gamji, a gidan sa dake Gamji a karamar hukumar mulkin Bakura.

Wannan yana kunshe a cikin takardar bayani wanda mai magana da yawun yansandan SP Muhammed Shehu ya rabawa manema labarai a garin Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Yace sun sami labarin wannan lamarin ne misalin karfe biyar na safe a ranar laraba, cewa da misalin karfe hudu da rabi na safen wadansu gungu mutane dauke da makamai sun yiwa gidan tsohon kwamiahinan kawanya inda suka shiga gidansa kuma suka sace diyan sa biyu,da wasu mutun biyu, da kuma jami’in tsaro na farin kaya, watau (Civil Defence). Kuma suka harbe mutun daya da raunata macce daya.

Yanzu haka dai, an baje jami’an ‘yan sanda a wurin inda suna can suna kokarin kubutar da wadanda aka sacen, da kuma kama masu laifin.

Rundunar yansandan taba tsohon kwamishinan, da kuma jama’ar wannan jihar tabbacin suna nan sunayin duk abinda ya kamata domin kubutar da wayanda akayi garkuwa dasu, kamar yanda sukayi a baya, inda suka kubutar da Uwayen kasar Ruwan Gizo, dana Basasa, da wasu mutane hudu ga hannun ‘yan bindiga a kananan hukumomin Bakura da Mafara.

Hakama anja hankalin jama’a da su daina yin fito na fito da ‘yan bindiga dadi, amma su rinka gaya wa hukumomin tsaro dake kusa da su domin daukar matakin nan take, don a kaucewa hasarar rayukka.

Idan dai baku mantaba, Alhaji Bello Dankande Gamji, ya taka rawar gani ta wajen yakar wadannan ‘yan ta’addan tun lokacin da yake shugaban karamar hukumar mulkin Bakura, inda ya sadaukar da rayuwar shi domin kare ‘yanci da mutuncin jama’arsa.

Hakama, lokacin da yake kwamishinan kananan hukumomi yayi duk abinda ya kamata, kuma ya yake su, inda sun sha kiransa ta waya su zage shi kuma su ce su ne ajalinsa, amma duk da haka bai ji tsoro ba domin yana kokarin yaga cewa an samu zaman lafiya a jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *