Daga: S-bin Abdallah Sokoto.

Shahararren dan wasan kwallon kafa dan asalin jahar Sokoto Abdullahi Shehu mai wasa a kungiyar Busaspor dake kasar Turkiya ya ziyarci filin wasa na Shehu Kangiwa Square a in da ya fara buga wasa kafin Allah ya daukaka shi zuwa Turai.

A lokacin ziyarar, Shehu ya gana da wasu daga cikin abokansa wadanda suka fara buga wasa tun suna yara, a in da ya baiwa wasu kyaututtukka kamar yadda muka sami labari.

Shehu, al’umma sun shaide shi mutun ne mai yawan kyauta, sannan gashi mutum wanda aka shaidi baida girman kai ko kadan.

Ubangiji Allah ya kara daga darajar duk wani mai tausayin al’umma a duk inda yake, ya kara yawaita irinsu a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *