Spread the love

Wa’adin farko na shugaban jam’iyar na kasa Uche Secondus zai kare a watan Disamban wannan shekara wata hudu masu zuwa kenan, kan haka ya fara neman yanda zai sake dare kujerar a wa’adi na biyu.

Kamar yadda wata majiya ta sanar da jaridar The Nation wasu jagororoin jam’iyar sun fara neman wanda zai maye gurbin shugaban saboda zaben 2023.

Gwamnoni da tsoffin ‘yan takarar shugaban kasa da wasu jagorori na kan gaba wajen ganin Secondus bai sake zama shugaban jam’iyar ba.

Duk da haka shugaban yana samun goyon bayan wasu shugabanni ciki har da gefen tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da wasu gwamnoni da ‘yan majaisar dokikin Nijeriya, da mafi rinjayen ‘yan majalisar zartarwa na jam’iyar PDP.

Majiyar ta ce ba abin mamaki ba ne in aka gano cewa Gwamnan Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Revers Nyesome Wike da wasunsu ba sa goyon bayan zarcewar shugaban jam’iya na kasa.

Ko mine ne dai wasu na ganin zai yiwu jagororin su zauna domin samun silhu gudun kar jam’iyar ta sake komawa cikin rikicin da ta fito a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *