Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

Rahotanni daga Unguwar Sheka da ke cikin birnin Kano na cewa, wani magidanci ya daure dansa dan shekara 31, tsawon shekara 15,
Matashin wanda mahaddacin Qur’ani amma mahaifinsa ya daure shi bisa wasu dalilin wanda shi kadai ya sansu,

Matashin ya samu yanci ne bayan da hukumar yan sandan kano ta samu rahoto akan lamarin, inda SP
Baballo Majia da DPO din Nassarawa suka jagoranci kubuto da matashin, inda yanzu haka yake asibitin Nassarawa domin kulawa da lafiyarsa.

A baya bayan nan ma dai an samu wani da aka tsare tsawon shekara 7, yanzu kuma ga wannan na shekara 15 duka a Kano, a jihar Kebbi ne dai aka fara samun wata da ta daure yaro dan kishiyarta a garken Awaki, masu lura da alamuran yau da kullum dai suna Allah wadai da irin wannan rashin Imani da ake yayi a halin yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *