Daga Mansur Isa Buhari.

Fannin ilmi na sahun gaba a fannonin da aka fi kokarin tallata kwazon Gwamnatin Jihar Sakkwato mai mulki a yau. To sai dai kuma bangaren ilimin manyan makarantun gaba da Sakandare da ke Jihar ne bangaren da ya fi kowane shiga cikin garari a dalilin riko irin na sakainar kashi da yake fuskanta daga hannun Gwamnatin.

Kamar takwarorinta sauran manyan makarantun da ke Jihar, Jami’ar Jihar Sakkwato wato Sokoto State University (wadda ita ce jami’a daya tilo mallakar Jihar) na fuskantar matsananciyar matsalar kanfar kudade wanda sannu a hankali matsalar ke ci-gaba da gurgunta al’amurranta.

Hukumar Gudanarwar Jami’ar na cikin halin kaka-ni-ka-yi na rashin kudade, hasalima wannan ne ya sa hatta aiwatar da ‘yan kananan ayyuka da kuma gyare-gyare a Jami’ar suke gagararta, wannan ne ya sa mahukuntan Jami’ar ke kai gwauro su kai mari da kokonsu na bara a tsakanin ofisoshi da gidajen ‘yan siyasa da wasu masu fada aji wajen kamun kafa domin ganin Gwamnati ta sakar musu wasu ‘yan kudaden da za su taimaka musu tafiyar da Jami’ar amma kuma sau da yawa kwalliya ba ta biyan kudin sabulu ba.

Ba da dadewa ba, a cikin daminar nan wani iskan hadari ya kware rufin wasu daga cikin gine-ginen jami’ar, amma sai da akwa kwashe makwanni kafin Hukumar Gudanarwar Jami’a ta iya aiwatar da gyaran wucin-gadi a wadannan wurare ta hanyar ‘yan dabaru, wannan kuwa ya faru ne ba domin komai ba sai domin tsabar azabar rashin kudade da Gwamnatin Jihar ta dade ta na ganawa Jami’ar.

Yanzu haka batun da ake yi, kamfanin da ke samar da jami’an tsaro ga Jami’ar da wanda ke samar da harkokin tsaftar muhallin tun-tuni suka tattara kayansu suka bar Jami’ar, haka su ma ma’aikatan wucin-gadi da leburorin da ke aiki a Jami’ar su ma guguwar ta yi gaba da su saboda tsawon lokaci an kasa biyansu dan ihsanin cikin cokali da a ke ba su a duk wata.

Yau kusan shekaru uku kenan rabon Jami’ar da samun ‘yan kudaden wata-wata da Gwamnati ke bayarwa ga hukumomi da ma’aikatunta a matsayin kudaden gudanarwa. Wannan ne ya sa yau fiye da shekara daya kenan, Jami’ar ta kasa gudanar da taron Majalisar Gudanarwarta saboda rashin kudi.

Da a ce abubuwa suna tafiya kamar yadda ya kamata, Jami’ar za ta iya yin amfani da ‘yan kudaden shiga da take samu daga kudaden makaranta da dalibai ke biya, akalla domin kula da ‘yan kananan bukatunta da suka kunshi samar da kayan aiki a ofisoshi, to sai dai kuma wannan ba zai yiwu ba saboda kashi 70 cikin 100 na daliban Jami’ar ‘yan asalin Jihar Sakkwato ne wadanda kudaden karatunsu zai haura naira miliyan 150 a duk shekara.

Sai dai kuma babu daya daga cikin wadannan dalibai da ke biyan ko sisi saboda Gwamnatin Jihar ce ke ikirarin daukar nauyin biya musu kudaden karatun, sai dai kuma Gwamnatin kan kasa wajen bayar da wadannan kudaden ga Jami’ar.

Ko bayan wannan tarnaki da Gwamnatin ta yi wa Jami’ar na rashin biyan kudaden karatun dalibai ‘yan asalin Jihar ta Sakkwato, hatta ‘yan kudaden da sauran dalibai ‘yan asalin wasu Jihohi ke biya, wadanda yawan daliban bai wuce kashi 30 cikin 100 na daukacin daliban Jami’ar ba, Gwamnati ta sanya Jami’ar mayar da kashi 60 cikin 100 na adadin kudaden cikin aljihun Gwamnati, ita kuma Jami’a ta rike kashi 40 cikin 100.

A takaice, mawuyacin halin rashin kudi da ke addabar Jami’ar Jihar Sakkwato ya kai matuka a wajen munana, al’amarin da ke matukar barazana ga gudanar da harkokinta, haka kuma matukar a ka ci gaba da rungume hannuwa ba tare da yin wata hobbasa ba, a ka ci gaba da nuna halin ko-oho ga wannan halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai da wannan jaririyar Jami’ar ke ciki, to babu shakka Jami’ar na gab da durkushewa musamman a harkokin karatunta.

Ina Mafita?

Matakin da Gwamnatin Jihar ke dauka na kaffa-kaffa da kudaden jama’a, wanda ke da manufar taka birki a kan yadda jami’an Gwamnati da sauran daidaikun jama’a ke yin rub da ciki a kan dukiyar al’umma, babu shakka mataki ne abin yabawa, duk da haka yana da kyau a aiwatar da wannan mataki tare da tabbatar da cewa muhimman ayyukan da ke bukatar daukar matakin gaggawa a hukumomi da ma’aikatu, musamman manyan makarantu ba su kasance a tauye ba, ko kuma su shiga cikin gagari.

Wancan tsarin raba kudaden shiga tsakanin makarantu da Gwamnatin Jiha yana bukatar a sake bitarsa, haka kuma wajibi ne Gwamnati ta tabbatar da tsarin sakin kudade kan kari kuma cikin sauri zuwa ga makarantun domin kaucewa yin gyaran gangar azbinawa!

Buhari, Malami ne a Jami’ar Usmanu Dan-Fodiyo dake Sakkwato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *