Spread the love

Daga Ibrahim Hamisu, Kano.

Rundunar ‘yan sanda na jihar Kano ta kubutar da wanda aka kulle a garejin motaa har tsawon shekara Bakwai.

A wata sanarwa da ya bayyana wa manema labarai, mai magana da hukumar ‘yan sanda ta jihar Kano, DSP Abdullahi ya ce a ranar 13/08/2020 da misalin Karfe 11:15 na dare, wani mutum mai suna Aminu farawa dan asalin jihar Kogi ya kulle dansa mai suna Ahmad dan shekara 30 na tsawon shekara 7, a garejin Mota da ke garin farawa dake karamar hukumar Kumbotso a nan Kano ba tare da kulawa ba.

‘yan sanda a bakin aiki.

Abdullah kiyawa ya kara da cewa “Mahaifin yaron ya ce shi fa ya kulle shi ne na tsawon shekara 3 saboda ya fara shaye-shaye,
Tuni dai hukumar ‘yansanda kubutar da shi kuma ta garzaya da shi asibitin Murtala don duba lafiyarsa,

Kwamisanan ‘yansanda na jihar Kano CP Habu A. Sani ya bada umarnin meka wannan Uba da yayansa da matarsa zuwa babban sashin bincike da ke Bompai don fadada bincike, kafin a mika shi zuwa Kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *