Spread the love

Babbar kotun shari’ar musulunci a jihar Kano ta yankewa tsoho dan shekara 60 hukuncin jefewa har sai ya mutu.

Kotun dake da mazauni a kofar kudu ta yanke hukuncin bayan zargin da ake yi wa Mati Audu da ya fito cikin al’ummar Falsa a karamar hukumar Tsanyawa ya yi wa ‘yar shekara 12 fyade laifin da ya musanya.

Alkalin da ya yanke hukuncin Ustaz Ibrahim Sarki Yola bayan da Mai laifin ya karba laifinsa har sau uku a zaman kutu daban daban.

Yola ya ce hukuncin yana cikin dokar da shari’ar musulunci ta tanadar na ajefe duk wani Mai aure da ya aikata laifin zina.

Wannan hukuncin ya zo kwana biyu bayan an yanke hukuncin kisa ga Yahaya Sharif Aminu da ya yi batanci ga manzon Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *