Spread the love

Daga Yusuf m. Nasir

Ba za mu yadda ba, Kuma ba zamu amince da cin amanar da ke shirin faruwa acikin Kwamitin daukar Ma’aikata(Special Public Works) wanda gwamnatin Tarayya za ta dauki Ma’aikata 1000 a kowacce karamar hukuma cikin kananun hukumomi guda 774 ba.
Ministan Ayyuka na Tarayyar Najeriya, Mista Festus Keyamo, ya nada Abubakar Muhammad General dan Jihar Kano, a matsayin ‘Publicity Secretary’ na Kwamitin Daukar ma’aikata Mutum 44,000 a jihar Kano.

Tun bayan nadin Abubakar General ya fara gudanar da ayyukan ofishin sa kamar yanda aka dora masa alhakin yin aiki bisa gaskiya da rukon amana. Sai dai Kash! Tun ba’aje ko ina ba ya fara samun turjiya daga wasu daga ciki ko kuma muce shugabannin kwamitin wadanda ba su yadda da bin tsari na doron gaskiya da yin aiki bisa qa’ida da kiyaye amanar al’ummar jihar Kano da aka basu ba.

A yanzu haka wadannan Mutane sun hada kansu su uku, sunyi amfani da damar da take hannun su na kula da amanar al’ummar Kano sun rubuta wata sabuwar WASIKA dake nuna cewa sun Watsar (Revoking) da wancan Appointment din da Minista ya bawa Abubakar General, yayin da suka ce sunyi ne da yawun Minista Festus Keyamo.

Ko da yake a Yanzu haka ana shirin kalubalantar wadannan mutane suke son yin amfani da wannan dama don son zuciyar su. Bayan zama da aka yi da dukkan ‘yan jaridu da lauyoyi da sauran masu rajin kare hakkin talakawa sun quduri aniyar bibiyar wannan lamari da nufin tunkarar shi Minista kai tsaye akan wannan kwamacala dake shirin faruwa a kwamitin da ya bawa amana. Kuma a shirye suke da su tona duk wata manuba da rashin gaskiyar da su wadannan mutane suke shirin aikatawa ta hanyar amfani da haqqin talakawa domin buqatun kawunan su.
Kuma daya Bayan daya al’umma za suji gaskiyar Lamari da sunayen wadannan mutane masu ci da gumin talakawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *