Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

A yaune babban kotu mai daraja ta hudu dake garin Gusau babban birnin jihar Zamfara ta yanke hukuncin rushe shuga bannin jam’iyar APC na jihar Zamfara, anan take ta bada umurnin shirya sabon zabe.

Da yake yanke hukuncin mai shara’a justice Bello Umar Gummi yace, bayan nazari mai zurfi da suka yi sun fahinchi cewa masu kara watau bangaren tsohon sanata Kabiru Garba Marafa na zargin an hanasu sayen takardun shiga zaben neman shugabanci ne inji daya bangaren na tsohon gwamna jihar ta Zamfara watau Hon, Abdul Aziz Yari Abubakar.

Ya kara da cewa duk da yake masu da’awar basu nuna wani abinda zaisa ace yayan jam’iyyane, amma hanasu sayen takardun neman shugabancin yajawo bangaranci a jam’iyar, kasan cewar suma yayan jam’iyya ne, adon haka mai shari’a yace ya zama cilas kowa a bashi yancinsa na shiga zabe, daga nan ya bada umurnin rushe dukkan shuga bannin kowane bangare.

Da yake tsokaci kan wannan hukuncin lauyan masu kara, Barista Misbahu Salawu yace, sun gamsu da wannan hukuncin, domin shirya sabon zabe shi zaiba kowane dan jam’iyya damar tsayawa yakara inhar yana bukata.

Ya kara da cewa, yanzu APC a jihar Zamfara batada shugabanni saidai wayanda za’a zaba nan gaba, yace kuma a shirye suke ga duk wani kalubale da zai iya biyo baya.

Shima a nashi bangare tsohon maiba APC shawara kan shari’a bangaren tsohon gwamna Jihar Zamfara watau Abdul Aziz Yari Abubakar, Barista Surajo Garba Gusau, yace wannan shari’a ce da wayansu mutane magoya bayan tsohon sanata Kabiru Garba Marafa suka shigar domin kawo matsala a jam’iyya.

Idan dai baku manta ba APC a jihar Zamfara ta tsinci kanta cikin rudanin shugabanci, tun shekara biyu da wata ukku da suka gabata, lokacin da akayi zaben sabbin shuga bannin dazasu jagoranci tafiyar tasu a wannan jihar.

Daga nan nefa aka samu shugabanni biyu, watau bangaren tsohon gwamna, a karkashin jagorancin Lawal M Liman gabdon Kaura, da kuma bangaren tsohon sanata Kabiru Garba Marafa, inda Alhaji Surajo mai katako ke jagoran ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *