Spread the love

 

Daga Mukhtar Halliru Tambuwal, Sokoto.

Sanannen mai tallafawa mabukata a jihar Sakkwato Alhaji Murtala Dan’iyan Jarman Sakkwato a karo na uku ya sake ba da tallafin magani ga bukatan jihar Sakkwato ta hannun hukumar Zakka da Wakafi ta jihar.

Honarabul  Isah Dan kasa ne ya jagoranci tawagar da ta kawo maganin a madadin Dan’iyan Jarma, an hannunta maganin ga shugaban hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki. 

Shugaban bayan ya karbi  maganin ya yi godiya da Addu’a ga wannan bawan Allah, ya kumayi Kira ga masu hali da su yi koyi da shi, a rika taimakon gwamnati ga irin wannan aiki a daina barin ta ita kadai, da wasu  daidaikun al’umma irin shi  a wannan aikin alkhairi. 

Shugaba Maidoki Sadaukin Sakkwato ya nuna matukar farincikinsa ga wannan bajintar domin shi ba wani abu da ya sa a gabansa kamar taimakon al’umma burinsa yanda yaro mai uba, ko babban mutum namiji ko mace mai arziki zai yi dariya don Allah ya hore masa yanda zai yi, haka yake son maraya da mabukaci ya zama ta hanyar taimaka masu a cikin al’umma.

Managarciya ta fahimci a duk sanda ka samu Sadaukin Sakkwato cikin damuwa da bacin rai, tau wata al’umma ce ya samu cikin damuwa, ba za ka samu ya yi farinciki ba har sai ya yi iyakar kokarinsa ga taimakonsu kuma an samu nasara.

 Shugaban ya hannun ta maganin ga maitaimakawa bangaren lafiya da ma’ajin na Hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *