Spread the love

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga mutanen Sakkwato su zama a fadake, wani mataki ne na kiyaye tsaron rayuwa da dukiyoyin jama’ar jihar.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wurin ta’aziyar rasuwar mahaifin dan majalisar dokokin jiha Alhaji Halilu Modachi mai wakiltar karamar hukumar Isa, ya ce a zama a fadake zai taimaki gwamnati a kokarin da take yi na samar da tsaro a jihar.

Tambuwal ya tsawatar kan daukar doka a hannu a lokacin da aka samu nasarar kama wandanda ake zargi da manyan laifuka a hannunta su ga jami’an tsaro mafi kusa don daukar matakin da ya dace, gwamnatoci a kowane mataki suna daukar matakin samar da mafita ga matsalar tsaron da ke addabar Nijeriya.  

Gwamna ya yi kira da a yawaita addu’a samun zaman lafiya da cigaban tattalin arziki a jihar Sakkwato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *