Spread the love

Sananan ‘yar wasan Hausa Fati Baffa Fage wadda aka fi sani da Fati Bararoji ta ce a yanzu ba ta da wani buri a rayuwarta kamar ta sake ganin ta yi aure a karo na biyu domin aure shi ne cikar kammalar ‘ya mace musulma.

Fati a hirarta da manema labarai ta ce abu ne na rayuwa da baka iya mallakarsa kamar rayuwa ce da mutuwa, ‘Na yi auren fari a bisa kaddara na rabu da mijina na haifi ‘ya daya, ina da burin sake yin aure, na cigaba da kasuwancina ba takura’.

Ta ce abu biyu ne ya sa ta bakinciki a rayuwa, karyar da aka yada ta rasu a hadarin mota, sai maganar aurenta wadda aka shirya komai kawayenta sun yi anko, an buga kalandar aure, an dauki wurin buki an shirya komai kawai sai ga maganar wanda zai aurenta ya fasa, ya je ya nemi wata ya aura, “Irin wannan abun yana iya sanya mutum zuciyarsa ta buga amma ni mayar da komai ga Allah a matsayina na musulma komai ya wuce.” A cewarta

Ta yi Magana kan zargin matan fim ba su zaman aure ta ce ba haka ba ne da yawan wasu mutane sukan zo wurinsu da wata manufa daban in ba su yi nasara ba sai su shigo da maganar aure bayan an yi sai su kawo wani uzuri da zai sa a rabu, ‘bai kamata a ga laifinmu ba domin wasu sun yi auren su zauna wadan da suka samu matsala kadan ne.’

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *