Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyar APC na Arewa maso yamma Barista Inuwa Abdulkadir da ya rasu bayan kwashe shekara 54 a duniya ya bar matan aure biyu da ‘ya’ya Tara,  an yi masa sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanadar an bizne shi a jihar Sakkwato. 
Rashin ganin jagororin jam’iyar APC na jihar Sakkwato  a wurin janazar ya ja hankalin mutanen da suka halarci wurin ganin ko ba komai yakamata aga tawagarsu don yana cikin shugabanninsu na kasa a lokacin rayuwarsa. 
Aminiya ta tuntubi shugaban jam’iyar APC na jihar Sakkwato Alhaji Isah Sadik Achida kan sanin dalilin rashin ganin fuskokinsu a wurin, amma magoya bayan jam’iyar PDP da shugabanninsu sun halarci wurin tare da mamaye gida da wurin bizne margayin, ya ce wannan lamarin da ya faru na rashin ganinsu abu ne da ya zo kawai ba da gangan ba ne. 
“Wannan abin da ya faru ba da gangan ba ne, ba don muna da matsala da wani ba ne, a san da abin ya faru jagoranmu Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Ahmad Aliyu Sokoto da  Minista Muhammad Mai gari Dingyadi duk suna Abuja.” a cewar Sadik Achida.
Shugaban ya cigaba da cewa shi kuma a lokacin da abin ya faru mahaifiyar amininsa ce ta  rasu suna wurin yi mata sutura don haka ne ya sa bai je ba.
“Muna yi masa rokon Allah ya gafarta masa ya sa ya huta, ba mu da wata matsala da kowa.” in ji Isah Achida. 
Al’ummar jihar Sakkwato sun ga laifin jagororin kan kin zuwa janazar kuma ba a ga wata tawaga da ta fito daga jam’iyar na,  a bangaren APC bayan Dan majalisar wakillai mai wakitar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela kusan ba wani jigo a jam’iyar da aka gani a janazar. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *