Spread the love

Kwamitin da gwamnatin Tarayya ta kafa domin ya bincike badakalar da ake zargin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Malam Ibrahim Maguy a tafka a jiya sun amince da shugaban kasa ya salami shugaban, kamar yadda wata majiya ta tabbatarwa jaridar daily trust.

Kwamitin wanda ke karkashin jagorancin tsohon shugaban kotun daukaka kara Alkali Ayo Salami sun gayyaci Magu a fadar shugaban kasa.

Wata majiyar da aka tabbatar ta ce kwamitin shugaban kasa ne ya kaddamar da shi don ya binciki zarge-zargen da ake yi wa Magu biyo bayan takakardar korafi da Ministan Shari’a Abubakar Malami da hukumar tsaro ta farin kaya suka gabatar ana zargin ya karkatar da dukiyoyin da ya kwato,  an jero laifuka 22 da ake zarginsa da su.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *