Spread the love

Jam’iayar APC ta fara tunanin wanda zai gaji tsohon shugaban jam’iyar na kasa Adams Oshiomhole wata majiya ta tabbatar da hakan.

“Gwamnoni da shugabannin jam’iyar suna duba wasu mutane don sanya daya daga cikinsu gaba, ciki akwai tsohon shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani da tsohon shugaban rosasshiyar jam’iyar ANPP Ogbonaya Onu.

“Har yanzu akwai wata hudu kafin jam’iyar ta yi zaben shugabanninta na kasa abin da aka fara shi ne sulhu kan ana son Kudu maso gabas(South East) ta fitar da shugaban domin yankin ne kawai a Kudancin kasar baya da yawan masu rike da mukamai a gwamnatin APC da jam’iyar.

“Wasu jagororin jam’iya ba su aminta da aba su shugabancin ba, domin rawar da suka taka a zaben 2015 da 2019 ba abar a zo a gani ba ce, ko an ba su mukamin shugaban jam’iya ba wani abu da zai canja a yankin, domin gidan jam’iyar PDP ne.”

Haka kuma alamu sun nuna kwamitin rikon kwarya na kasa zai saukar da shugabannin jam’iyar a wasu jihohi saboda rikicin da suke ciki. Sai da wasu gwamnoni na kokarin ganin an saukar da dukkan shugabannin jam’iyar a jihohi 36 abin da ake ganin zai taimaki jam’iyar ta dawo da karfinta.

Wata majiyar na cewa ko an fita batun maganar wasu gwamnoni, jam’iyar na tare da nauyi tun daga mazaba har matakin jiha.

Ba abu ne mai yiwu ba za a yi taron kasa mambobin jam’iya ba su zabe wadan da za su wakilce su ba, akwai bukatar gyara wannan kalu bale.

Wasu na ganin matsalar in da take a saukar da duk jihar da ke da rikicin shugabanci da aka kasa daidaitawa, wadan da ke lafiya lau su zabi wadan da za su wakilce su a taron kasa.

Mataimakin sakatare na jam’iya Yekini Nabena ya ce in sun kai ga wannan lamari za su sanar da jama’a.

Managarciya na ganin matukar jam’iyar na son samun nasarar dunkewa wuri daya su cimma bukatarsu sai sun fara daga kasa a sauke kowa dukkan shugabanninta a jihohi 36, a ba da rikon kwarya a zabi sabbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *